Yaro da ake zargin an daure tare da tumaki har shekara 2 a Birnin kebbi, gaskiyar lamarin

Ranar Lahadi 9 ga watan 8 2020 da misalin karfe 2:40 'yan sanda suka sami labarin wani yaro mai suna Jibrin Ali mai kimanin shekara 11 da ke unguwar Badariya cikin garin Birnin kebbi, cewa mahaifinshi ya daure shi da igiya a gidansu tare da tumaki a Turaku har tsawon shekara biyu.


Sakamakon haka jami'an yansanda rundunar shiyar garin Birnin kebbi suka je wajen kuma suka kubutar da yaron daga halin da yake ciki a gidan. Daga bisani suka kai yaron Asibitin Sir Yahaya da ke garin Birnin kebbi domin samun magani.


Bayan jami'an yansanda sun fara bincike, ISYAKU.COM ya gano cewa yansanda sun gane cewa zai iya yiwuwa yaron na da matsalar tabin hankali bisa bayyanar lamarinsa a zahiri, sakamakon haka mahaifinsa ya yi kokarin kai shi Asibitin masu tabin hankali da ke garin Jega a cikin jihar Kebbi da Asibitin masu tabin hankali da ke garin Kware a jihar Sokoto kamar yadda Kakakin hukumar 'yansandan jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar ya shaida wa manema labari.


ISYAKU.COM ya samo cewa bayan da abin ya ci tura, sai mahaifinsa ya dauki wannan mataki na daure shi a gida, gudun kada ya tafi yawace-yawace kuma a yanayi na rashin lafiyar tabin hankali sai mahaifin ya daure shi a gida domin kada wani abu ya cutar da shi wajen yawo.


Jibrin Aliyu
Amma duk da haka, mahaifinsa mai suna Aliyu Umar, da sauran kishiyoyin uwar yaron masu suna Rabi Aliyu, Fatima Aliyu da kuma Aisha Muhammad Aliyu, matan shi mahaifin yaron, suna hannun 'yansanda domin amsa tambayoyi da bincike kan lamarin. Ainihin mahaifiyar yaron Allah ya yi mata rasuwa kenan bata gidan.


Binciken ISYAKU.COM ya gano cewa shugaban Asibitin Sir Yahaya da ke Birnin kebbi inda yaron ke samun kulawan Likitoci, watau Dr. Aminu Bunza, ya dauki alkawarin zai kula da yaron da kuma lafiyarshi har tsawon wata hudu domin a tabbatar ko tabin hankalin ne ko wata lalura ce ke tattare da wannan yaro sakamakon yanayi da yake ciki a bangaren lafiya .

Dr Aminu Bunza ya dauki nauyin kula da Jibrin Aliyu har wata hudu


Sakamakon bincike da babban Likita Dr. Aminu Bunza, da kuma kulawa da zai ba yaron na tsawon wata hudu ne kadai zai iya warware gaskiyar lamarin wannan yaro, kasancewa mahaifinsa ya yi ikirarin cewa yaron yana da lalurar tabin hankali ne shi ya sa ya daure shi domin kare lafiyarsa.

Makwabta da Lauyoyin kare hakkin bil'adama ne suka bankado lamarin


ISYAKU.COM ya gano cewa makwabtan mahaifin Jibrin ne suka kai rahotu zuwa ofishin kare hakkin bil'adama a garin Birnin kebbi, watau National Human Rights Commission karkashin wakilinta na jihar Kebbi Barr. Hamza Attahiru Wala, NHRC bata je gidan ita kadai ba sai suka je tare da jami'an 'yan sanda daga rundunar 'yan sanda na Birnin kebbi.


A cikin tawagar hukumar kare hakkin bil'adama har da kungiyar Lauyoyi mata na Duniya, tare da wakilinsu na jihar Kebbi Barr. Amina Ka'oje, tare da wakilin kungiyar kare hakkin bil'adamana Duniya  a jihar Kebbi Barr. A.A Fingilla da sauran Lauyoyi.

Jin kai ne ko mugunta, mahaifin Jibrin ya daure shi tare da dabbobi, amma yana da mata uku suna da dakuna a gidan


Jami'an yansanda sun sami yaron daure ne a turaku tare da dabbobi a yanayi mai ban tausayi lokacin da suka isa gidan.  Ko wannan ne kariya da mahaifin Jibrin watau  Malam Aliyu Umar yake ikirarin cewa yana ba dansa Jibrin Aliyu domin kada ya illata kansa ko wani abu ya cutar da shi wajen yawace-yawace kuma ga tabin hankali ?, babu daki ne a gidan, duk da cewa mahaifin Jibrin yana da mata uku, kuma kowace da dakinta a gidan ? .

Gaskiya da darasi da ya kamata a gane a wannan lamari

Sakamakon bayanai da ISYAKU.COM ya tattaro sun bayyana cewa:

1- Mahaifin Jibrin ya ce ba ya daure shi ne domin mugunta ba, domin ya yi ikirarin cewa ya kai shi Asibitin kula da masu tabin hankali a garin Jega , da garin Kware a jihar Sokoto da niyyar sama masa magani, amma lamarin ya fi karfinsa.

2- Mahaifin Jibrin ya daure shi tare da dabbobi a turaku, amma yana da mata uku, kuma kowace tana da dakin kwana, babu wani daki da zai sa Jibrin domin samun kulawa ingantacce?

3- Wane kokari yan wa, abokan arziki, da makwabta suka yi domin taimaka wa lalurar Jibrin kafin mahaifinsa ya kai ga daure shi tare da dabbobi?.

4- Idan mahaifinsa ya daure Jibrin ne saboda kada ya raunata kanshi ko wani lamari ya cutar da shi wajen yawace-yawace sakamakon tabin hankali, wannan zai zama dalili na rashin samun kulawa wajen abinci da tsabtar rayuwa ga Jibrin ?

Rahotun Isyaku Garba Zuru

Mawallafin Shafin ISYAKU.COM

Domin karin bayani ko kalubale kan wannan rahotu LATSA NAN


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN