'Ta'addanci ne': Cacar baki ta kaure a kan hukuncin kashe matashi saboda batanci ga Annabi

Wasu 'yan Najeriya sun mamaye dandalin sada zumunta domin bayyana ra'ayinsu da nuna fushinsu a kan hukuncin kisa da wata kotun shari'ar Musulunci ta zartar a kan wani matashin mawaki.

A ranar Litinin ne wata babbar kotun Shari'a da ke zamanta a Hausawa Filin Hockey da ke cikin birnin Kano ta zartar da hukuncin kisa a kan matashin mai shekaru 22 saboda wallafa wata waka mai dauke da kalaman batanci ga Annabi Muhammad.

Daily Ngerian ta wallafa cewar wata jaridar yanar gizo mai suna 'Focus' da ke Kano ta bayyana cewa alkalin kotun, Khadi Aliyu Muhammad, ya zartar da hukuci a kan matashin, Yahaya Aminu Sharif, da safiyar ranar Litinin.

Jaridar ta bayyana cewa Khadi Muhammad ya zartar da wannan hukunci ne bayan ya gamsu da hujjojin cewa matashin ya aikata laifin da ya jawo aka gurfanar da shi a gaban kotun.

An zargi mawakin da daukaka shugaban darikar Tijaniya a kan Annabi Muhammad - lamarin da ya fusata jama'ar birnin Kano har su ka yi zanga-zanga. Duk da matashin bai musanta tuhumar da ake yi ma sa ba, Khadi Muhammad ya ce mawakin Yahaya zai iya daukaka kara.

Batun hukuncin kisan ya jawo barkewar cece kuce da musayar yawu a tsakanin 'yan Najeriya a dandalin sada zumunta, musamman shafin manhajar Tuwita.

Wani ma'abocin amfani da dandalin Tuwita ya bayyana cewa; "babu wurin da aka ambaci irin wannan hukucni a ciki Qur'ani da Hadisai, a sa"zartar da hukuncin kisa saboda batanci bashi da banbanci daga kisan jama'a da sunan 'arna'.

Kisa saboda batanci bashi da maraba da ta'addanci." Shi kuwa wani mazaunin Kano mai suna Khalil cewa ya yi; "babu wanda za a kashe saboda batanci a Najeriya, sai wanda ya ga dama.

Shari'ar Musulunci ba ta da gurbi a kasa kamar Najeriya wacce ke amfani da kundin tsarin mulki da ba ruwansa da addini. Shi kuwa wani ma'abocin amfani da dandalin Tuwita cewa ya yi; "babu wanda ya kamata a kashe saboda wani furuci, a saboda haka zartar da wannan hukcuci ya nuna cewa har yanzu babu cigaba a kasar nan.

"Zartar da hukuncin kisa saboda batanci tamkar take hakkin bil'adama ne, ya zama dole gwamnatin tarayya ta hana kaddamar da wannan hukunci," a cewarsa

Source: Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN