Rikicin da ya mamaye jam'iyyar PDP reshen jihar Ekiti ya kara tsamari a ranar Asabar, sakamakon rabewar jam'iyyar gida biyu, inda kowanne bangare ya zabi shuwagabannin sa.
Jam'iyyar PDP ta kasance cikin rabuwar kai a 'yan kwanakin nan, sakamakon rashin jituwar da ta shiga tsakanin Sanata Biodun Olujimi da Mr Ayo Fayose.
Sanata Biodun dai ita ce mai wakiltar mazabar Ekiti ta Kudu a majalisar dattijai, yayin da Mr Ayo shine tsohon gwamnan jihar, lamarin da ya jawo rabuwar kai a jam'iyyar.
Rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa ne ya tilasta kwamitin shugabancin jam'iyyar na kasa (NWC) a kafa kwamitin rikon kwarya na mutane bakwai da zai jagoranci jam'iyyar a jihar.
Kwamitin rikon kwaryar na karkashin shugabancin tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattijai, Sanata Hosea Agboola.
A taron zaben jam'iyyar da aka gudanar a ranar Asabar, tsohon kwamishin muhalli na jihar, Hon. Bisi Kolawole ya samu nasarar zama shugaban jam'iyyar daga inuwar Fayose.
Sai dai, a bangaren Olujimi, itama ta fitar da tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Kehinde Odebunmi a matsayin shugaban jam'iyyar.
Tawagar Fayose ta gudanar da zabenta a kan idanun tsohon gwamnan jihar, Segun Oni, a ginin baki na Petim, da ke a gidan baki na Lotus, babban birnin jihar.
Fayose ya gargadi mambon jam'iyyar da su kauracewa rashin da'a da biirewa umurnin jam'iyya, yana mai cewa an zalunci PDP a zaben 2018, amma 2022 na nan zuwa don daukar fansa.
Source: Legit
Source: Legit
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/