Wani matshi mai suna Yusuf Salisu Buzu, ya roki Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, domin ya gyara masu hanyar Koko zuwa Zuru, ita kuma Gwamnatin tarayya ta biya shi.
Salisu Buzu ya ce " Mai girma Gwamnan jihar Kebbi, ka taimaki al'umman Zuru, ka yi masu hanyar Koko zuwa Zuru, Gwamnatin tarayya ta biya ka. Kamar yadda ka saba faranta rayuwar al'ummaka".
"Mai girma gwamnan jahar kebbi Sen.Atiku Abubakar Bagudu (Matawallen Gwandu) ka taimaki al-ummar zuru ka faranta masu rayuwa kamar yadda ka saba faranta rayuwarka na jahar kebbi.
Babu shakka al-ummar jahar Kebbi suna cikin al-ummar da suka more romon dimukradiyya, sakamakon irin yadda gwamnatin jahar Kebbi take kyautatama al-umma ta bangare daban daban, kama daga kiwon lafiya, ayukka, noma, samarda aiki ga al-umma da dai sauran abubuwan more rayuwa.
Amma mai girma Gwamna kasan "Yan adam ajizai ne, duk da irin kokarin da kakeyi ba zamu barka hakanan ba, sai mun kara maka aiki duba da muna da tabbacin kai maijin kukan talakkawan ka ne.
Mai girma gwamnan jahar kebbi ka taimaki al-ummar Zuru da hanyar Koko zuwa Zuru. Wallahi al-ummar Zuru suna cikin al-ummar da suka nuna soyayya gareka".
Daga Yusuf Salisu Buzu
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/