Wasu masu fafutika sun ƙona Al-Kur'ani mai tsarki a garin Malmo na ƙasar Sweden, abin da ya jawo zanga-zanga tare da tashin hankali ranar Asabar.
Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito masu zanga-zangar kusan 300 sun cinna wuta a kan tituna tare da jefa abubuwa a kan 'yan sanda a daren Juma'a.
An ƙona Kur'anin ne da tsakar ranar Juma'a a kusa da wata unguwa ta 'yan cirani da wasu masu tsaurin ra'ayi suka yi sannan suka wallafa bidiyon a intanet, a cewar kamfanin dillancin labarai na TT.
AP ya ce an kama mutum uku bisa zargin haddasa ƙiyayya ga wani rukunin al'umma ta hanyar ƙona Kur'ani - littafin da al'ummar Musulmi ke girmamawa a matsayin mai tsarki
Source: BBC
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/