Shin ko bauɗewar babban yatsan ƙafa gado ne?

Bauɗewar ko karkacewar babban yatsan ƙafa da a ke cewa "hallux valgus" a likitance na daga cikin matsalolin da kan shafi tafin sawu.

Wannan matsala na faruwa ne yayin da babban yatsan ƙafa ya karkace zuwa yatsa na biyu sakamakon canje-canje a tantanai (jam'in tantani) da ke riƙe da ƙasusuwan babban yatsa. Sai dai, wannan matsala ta fi bayyana ga mata.

Daga cikin abubuwan da ke kawo matsalar sun haɗa da:

1] Gado: Kaso mai yawa na masu bauɗaɗɗen yatsan ƙafa suna gadonsa ne ta ɓangaren uwa ko uba. Haka nan masu shimfiɗaɗɗen tafin sawu wato "flat foot" a turance, na da ƙarin haɗarin samun bauɗaɗɗen babban yatsan ƙafa.
2] Bayan samun wannan matsalar ta hanyar gado, ana samu ta hanyar sanya matsatstsen takalmin da ke matse yatsun ƙafa sosai, kamar takalmi coge. Sanya irin waɗannan takalma yau da kullum kan haddasa canje-canje a tantanai da tsokokin da ke riƙe da babban yatsan ƙafa. Saboda haka, akwai buƙatar sanya takalmi mai yalwataccen masakar yatsun ƙafa.
3] Ciwon kumburin gaɓɓai, kamar ciwon amosanin gaɓa (osteoarthritis), ciwon sanyin ƙashi (rheumatoid arthritis), ciwon gawut (gout arthritis), da sauransu.

Alamomin bauɗewar babban yatsan sun haɗa da:

1) Bauɗewar babban yatsan ƙafa zuwa yatsa na biyu.
2) Bayyanar kanta, wani lokacin tare da kumburi, a gefen maɗaukar babban yatsan.
3] Ciwo tare da kumburi a dai-dai kantar babban yatsan ƙafa.
A yayin da kake / kike fama da irin wannan ciwon yatsan ƙafa, tuntuɓi likitan fisiyo domin duba ka / ki da bayar da shawarwari kan yadda za a shawo kan matsalar.

Source: Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post