Yadda 'yan daban daji suka kashe abokina - Labarin Matashin da ya tsallake rijiya da baya

Mahara da ake zargi ‘yan daban daji ne, sun kashe wani mutun a harin da suka kai kan al’ummar Kona, wani kauye da ke wajen Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

An ruwaito cewa masu tayar da zaune tsayen sun kai harin ne a daren Litinin, inda suka rika harbin kofofin gidajen mutune da zummar ganin bayan duk wanda ya fito. Haka kuma sun jefa al’ummar cikin halin ha’ula’I yayin da suka rika cinna wuta a gidajen mutane.

Daya daga mazauna kauyen da ya tsira da harbin bindiga, Silas Dame, ya zayyana yadda maharan suka kashe wani abokinsa. Yayin zantawa da manema labarai na gidan talbijin din Channels, Silas ya ce bai gane fuskar ko mutum daya daga cikin ‘yan ta’adan ba, abin da kawai zai iya tuna wa shi ne kowanensu yana rike da bindiga.

“Da misalin karfe 12.00 na dare a ranar Litinin bay an duk ‘yan gidanmu sun yi bacci, sai na farka yayin da naji motsin taku da kafa kuma kwatsam sai harbin bindiga ya biyo baya.”

“Ba mu da masaniyar ko su waye. Sun rika bi gida-gida suna kwankwasa kofofi kuma duk wanda ya fito su harbe shi.”“Duk bukkar da ba a bude ba sai su cinna mata wuta.”

“A haka suka kashe abokina bayan an kwankwasa kofa kuma ya bude cikin hanzari inda nan take suka batar da shi, amma ni na tsira da rauni na harbin bindiga.”

A nasa bangaren, kwamandan 'yan sintiri a yankin, Alli Kotonu, ya yi bayanin cewa sun yi tunkari 'yan bindigar wanda hakan ya tilasta su tsere. "Mun yi musayar wuta kuma yayin da suka gano tabbas zamu yi galaba a kansu, sai suka sulale ta cikin dokar daji.

Sai dai babban takaicin shi ne yadda suka samu nasarar kashe wani mazauni daya daga cikinmu.” Yayin da aka tuntubi jami'in hulda da al'umma na rundunar 'yan sandan jihar Taraba, David Misal, ya ce ba ya gari sakamakon wani aiki da ya fita aiwatar wa a wajen jihar.

Sai dai ya tabbatar da cewa jami'an 'yan sanda sun bi sahun maharan da manufar cafke su domin su fuskanci hukunci daidai da abinda suka aikata.

Source: Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post