Matawalle zai fara yankewa masu tukin ganganci hukuncin kisa bayan mutuwar wasu...

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya ce gwamnatinsa za ta kafa hukuncin kisa ga direbobi masu tukin ganganci a jihar. Ci gaban na zuwa ne bayan mutuwar magoya bayansa 15 a wani hatsarin hanya bayan sun yi masa maraba da zuwa karamar hukumar Tsafe.


Hatsarin ya afku ne lokacin da wata babbar mota ta kwace sannan ta je ta daki ayarin motoci hudu na magoya bayan Matawalle a hanyar Gusau-Funtua da ke Tsafe.


A cikin wani jawabi a ranar Asabar, Yusuf Idris, daraktan labarai da waye kan jama’a na gwamnan, ya ce za a samar da hukuncin kisa a matsayin matakin hukunta direbobi masu tukin ganganci. Idris ya ce gwamnan ya yanke wannan hukunci ne lokacin da ya jagoranci mambobin majalisarsa da hukumar kamfanin BUA a wani ziyarar jaje da suka kai fadar Ibrahim Bello, sarkin Gusau, kan mutuwar mutum 15.


Ya ce sabuwar dokar za ta tabbatar da ganin cewa an tilasta wadannan direbobi biyan diya a kan duk wani raid a aka rasa. Matawalle ya sanar da bayar da gudunmawar naira miliyan 2 ga kowani iyali na mamatan wadanda ked a mata, naira miliyan 1.5 ga iyalan mamatan da basu da mata.


Ya ce za a saka magajin kowani mamaci a cikin jerin wadanda jiha za ta dunga biyan alawus din N50,000 duk wata har zuwa karshen wa’adin mulkinsa. Gwamnan ya kara da cewar gwamnatinsa za ta samar da iyakar gudun da motoci za su dunga yi a manyan titian, ma’aunin kayayyaki kan manyan motoci. Za kuma a dunga yi wa direbobin gwajin kwaya domin hana tukin ganganci, wanda ke yawan haifar da mace-macen rayuka.Matawalle ya ce sabuwar dokar zai tabbatar da ganin cewa direbobi sun dandana kudarsu na daukar rayuwan jama’a a jihar. Ya bukaci shugabannin kamfanin BUA da su ja wa direbobinsu kunne a kan adadin gudu da aka amincewa masu tuki su yi.


A nashi jawabin, Aminu Suleiman, Shugaban tawagar kamfanin BUA, ya ce tawagar ta zo yin ta’aziyya ne ga gwamnati, masarautar Gusau, mutanen jiha da kuma iyalan wadanda aka kashe sakamakon wani hatsari da ya cika da direban kamfanin.Sarkin ya yaba ma Matawalle da kamfanin BUA kan kulawarsu, inda y ace dukkan mai rai mamaci ne. Ya kara da cewar za a yi amfani da gudunmawar da aka bayar sosai ta yadda ya dace.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt


Previous Post Next Post