Ko me ke kawo shanyewar ƙafafu ga wasu matan bayan haihuwa?

Daga cikin matsalolin da iyaye mata kan fuskanta yayin naƙuda da ke hana su tafiya saboda raunin ƙafafu akwai matsalar nan da ake cewa "Maternal Obstetric Palsy" a turancin likita.

Wannan matsala na faruwa ne yayin naƙuda a lokacin da kan jariri ya sauko zuwa ƙugun uwa.

Tsawaitar naƙuda ko kuma tangarɗar naƙudar kan sa kan jariri ya danne gungun jijiyoyin laka da suka sauko zuwa ƙugu da ƙafafu da ake cewa "Lumbosacral Plexus" a yaren likita.
 
Duk da cewa wannan matsala tana iya shafar ƙafafu biyu a lokaci guda, amma tafi shafar ƙafa ɗaya.

Iyaye mata da suke da haɗarin samun wannan matsala sun haɗa da:

1] Gajeru; saboda ƙuncin ƙugu da su kan zo da shi.
2] Naƙuda / haihuwar jaririn da kansa ya wuce matsakaicin girma, wato girman kan jaririn ya fi faɗin mafitar ƙugun.
3] Nawa ko tsawaitar naƙuda fiye da yadda aka saba.
4] Uwayen da suka gaza haihuwa da kansu har sai da aka temaka musu da maƙatar ungozoma domin zaƙulo kan jaririn, wato "forcep delivery" a turance.
5] Juyewa ko karkacewar jariri yayin naƙuda da sauransu.

Alamun larurar sun haɗa da:

Waɗansu alamun suna bayyana tun a lokacin naƙuda, a yayin da wasu kuma kan bayyana bayan haihuwa.

1] Ciwo daga cinya zuwa tafin sawu.
2] Rashin jin daɗi a fatar ƙafar; kamar jin tafiyar kiyashi, jin dindiris, jin kamar ana tsira allura, ko kuma jin kamar jan wutar lantarki.
3] Shanyewar ko raunin kafafu da tafin sawu.
4] Ƙwacewar fitsari da/ko bahaya.
5] Matsalar saduwa da iyali, da dai sauransu.

Sai dai, sau da yawa a kan bar iyaye matan da suka haihu a kwance saboda sun kasa tashi sakamakon rashin ƙwarin ƙafafunsu ba tare da an ɗauki matakan da suka kamata ba.

A yayin da mace ta haihu, sannan aka lura ta kasa taka ƙafafunta a tuntuɓi likitan fisiyo domin ɗaukar matakan da suka kamata.

Source: Physio Hausa

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN