Duba illolin shan taba sigari

Shan taba sigari na daga cikin matsalolin da suka fi lashe rayukan mashaya tabar. Kuma duk cikin mashaya taba biyu, ɗaya daga cikinsu kan mutu ne sakamakon cutukan da shan tabar ke jefa su.

Shan taba sigari na da gagarumar illa ga dukkan sassan jiki kamar haka:

1. Zagayawar jini: Kamar yadda aka sani ne cewa; zagayawar jini shi ne ci gaban rayuwa. Sai dai, yayin da gubar da ke ɗauke cikin hayakin taba sigari ta shiga cikin jini hakan zai sa:
i. Kaurin jini ya ƙaru, wannan zai ƙara haɗarin daskarewar jini a cikin jijiyoyin jini.
ii. Ƙaruwar hauhawar jini da ingiza bugawar zuciya fiye da ƙima; wannan zai ƙara wa zuciya wahalar harba jini zuwa sassan jiki.
iii. Cushewar ko matsewar jijiyoyin jini; wannan zai rage wa sassan jiki samun isashshen jini da iskar oksijin.

2. Lahanta huhu: Huhu wanda nan ne sashin da ake canjin iska tsakanin iskar oksijin (oxygen) da muke shaƙa da kuma iskar kabon (carbondioxide) da muke fitarwa. Shan taba sigari na rage wannan aiki na canjin iska, baya ga lalata tanadin kariya da Allah ya shirya wa huhun, wannan zai karya garkuwar huhun ta yadda cutukan numfashi kamar tarin fuka (TB), kumburin kwaroron huhu, daji / kansar huhu za su kama mutum cikin sauƙi.

Waɗannan illoli na shafar dukkan sauran sassan jiki kamar zuciya, jijiyoyin jini, kayan ciki, fata, ƙashi da raguwar ƙwayoyin halittar haihuwa da dai sauransu.

3. Jinkirin warkewar karaya: Muggan sinadaren da suke cikin hayaƙin taba na hana ƙwayoyin halittar ƙashi hayayyafa ko tsatstsafowa da wuri bayan karayar ƙashi domin samun haɗewar gurbin karayar.
Wannan ya sa masu shan taba sigari ke samun ƙarin tsawaitar lokacin da karaya ya kamata ta warke, ko kuma rashin haɗewar ƙashin ma ɗungurungum.

4. Lahani ga ido: Taba sigari na lahanta ido kamar yadda take lahanta huhu.
i. Duk da alaƙar da ke akwai tsakanin shan taba sigari da makanta, mutum ɗaya cikin biyar ne kawai ke da masaniya kan hakan.
ii. Mashaya taba na da ninki biyu na haɗarin rasa ganinsu fiye da waɗanda ba sa sha.
iii. Hayaƙin taba na ɗauke da muggan sinadaran da ke tunzira ko lahanta ido.
iv. Misali, muggan ɓirɓishin ƙarafe nau'in "lead" da "copper" na iya taruwa a gilashin ido (eye lens) su kuma kawo larurar dindimin ido.
v. Shan taba sigari na ta'azzara ciwon idon da ciwon siga ke kawowa ta hanyar toshe jijiyoyin jinin ido.
vi. Kuma mashayan taba na da ninki goma sha shida fiye da marasa sha na haɗarin makanta sakamakon toshewar jijiyoyin jinin ido.
vii. Shan taba na da haɗarin ta'azzara ko janyo matsalolin gani wanda ya zama wajibi mashayan su ƙaurace mata.
A taƙaice dai, bayan duk ɗinbum illolin shan taba sigari, duk wata cuta ko larura shan taba sigari na da tasirin ta'azzara ta.

Source: Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN