A wasikar da ya aike masa ranar 5 ga Agusta bisa wani kara da lauyan yan majalisar, West Idahosa, ya shigar, Malami ya ce akwai bukatar bada tsaro domin hana barkewar rikici a Edo. Yan majalisan 17 dake goyon bayan dan takaran jam'iyyar APC, Fasto Osaze Ize-Iyamu, sun kasance cikin rikici da takwarorinsu bakwai dake goyon bayan gwamnan jihar Godwin Obaseki.
A jiya mun kawo muku rahoton cewa 'yan majalisu 17 na majalisar dokokin jihar Edo, da suka hada da mambobi 12 da a baya aka bayyana kujerarsu a matsayin wofi, sun yi ikirarin cewa sun tsige kakakin majalisar jihar, Francis Okiye, da mataimakinsa, Roland Asoro. Sun yanke wannan hukuncin ne a ranar Alhamis a wani boyayyen wuri a Benin City, babban birnin jihar, awanni bayan da jami'an tsaro suka mamaye zauren majalisar.
A bangarensu, sunce sun nada Victor Edoror, mai wakiltar mazabar Esan ta tsakiya, da Emmanuel Agabje, daga mazabar Akoko-Edo II a matsayin kakakin majalisar da mataimakinsa.
A wajen taron, 'yan majalisu 12 da aka zabe su, an rantsar da su tare da sauran 'yan majalisun 5 wadanda suka yi mubayi'a ga Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC, suka ce sun tsige kakakin.
Majalisar dokokin jihar Edo ta kasance cikin rikici tun a shekarar 2019, wacce ta sake rikicewa a yanzu a yayin da ake shirye shiryen zaben gwamnan jihar. An zabi 'yan majalisu 24 daga mazabu 24 na jihar a babban zaben 2019. Sai dai, 10 daga cikinsu, an rantsar da su ne a ranar 17 ga watan Yulin shekarar, lamarin da ya jawo zaune-tsaye.
Source: Legit
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/