Duba dalili da abin da ke sa bayanka ya amsa idan ka dauki abin nauyi

Daga cikin raunukan da kan faru a gadon baya musamman yayin ɗauka ko ɗaga kayan nauyi akwai cirar nama ko tsinkewar naman gadon baya. Cirar nama ko tsinkewar nama na faruwa ne yayin da danƙon naman ya ƙure, ma'ana, talewa ko ɗamewar naman to wuce ƙa'idar ɗamewarsa, ko kuma ƙarfin nauyin kayan ya rinjayi ƙarfin da tsokar za ta iya bayarwa bayan ta yunƙura.

A yayin da aka samu wannan matsala, gadon baya zai amsa, sannan matsanancin ciwo ya biyo baya nan take, saboda cirar nama ko tsinkewar nama a wani sashi na tsokokin gadon baya.

Alamun cirar nama / tsinkewar naman gadon baya sun haÉ—a da:

1. Wasu lokutan a kan ji sautin "É—as" a daidai lokacin da aka É—aga nauyin, biyo bayan tsinkewa ko yagewar sashin tsokar gadon baya.

2. Matsanancin ciwo nan take, musamman idan aka sake yunƙurin motsa wurin.
3. Kumburi a wurin raunin.

4. Borin tsoka (muscle spasm) - tsokar wurin kan yi damƙa ko ta riƙa mommotsawa da kanta akai-akai, wanda hakan ke haifar da ciwo ko rashin jin daɗi a wurin raunin.

5. Raguwar aikin gaɓɓan da raunin ya shafa, misali, a kan ji ciwo yayin sunkuyawa, sunkuyawar gefe ko gantsarewa wanda hakan zai sa a riƙa kauce wa irin wannan motsi saboda ciwon.

Da zarar ka samu irin wannan matsala a gadon baya ko sauran gaɓɓai, tuntuɓi likitan fisiyo domin jinyar raunin, har da ma ba ka shawarwari kan matakan kariya don kauce wa faruwar hakan nan gaba.

Source: Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN