Bidiyon yadda mai renon jariri yar shekara 50 ta dinga marinsa domin ya dameta da kuka

Wani hoton bidiyo da aka dauka a asirce ya nuna yadda wata mai renon jarirai mai suna Wang Mou yar shekara 50 a Duniya ta dinga marin wani jariri da take reno a kafafu, duwawu da cikinsa domin ya dameta da kuka.

Mahaifin jaririn mai shekara 26 ne ya nada bidiyon yadda mai renon ke ta marin jaririnsa ta hanyar yin amfani da manhajan tsaro da ya sauke a wayarsa.

An gan yadda mai renon jaririn ta dinga marin kafafu da sauran sassan jaririn a hoton bidiyon da mahaifin jaririn Mr.Tian ya nada a birnin Shahe da ke gundumar  Hebsei na gabas a kasar China.

Yan sanda sun fara gudanar da bincike bayan Mr. Tian ya shigar da kara a gabansu.

Kalli bidiyo a kasa:Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post