• Labaran yau


  Akwai masu zagon kasa wajen yaki da boko haram kuma ba a son Buhari ya sani - Zulum

  Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum wanda ya ketare rijiya da baya sakamakon harin bazata na bako haram kan ayarinsa, ya yi zargin cewa akwai zagon kasa a tsarin yaki da boko haram da ake yi wanda ba a son shugaba Muhammadu Buhari ya sani a yankin gabas maso arewa.

  Gwamanan ya yi wannan zargin ne bayan ziyarar jaje da Gwamnonin Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da na Jigawa Badaru Abubakar suka kai masa ranar 2 ga watan Agusta kan hari da aka kai masa.

  Zulum ya yi zargin cewa akwai wadanda ke kokarin kawo cikas kan nassararori da Gwamnati ta ke samu wajen fada da boko haram, kuma shi ya sa har yanzu yakin ya ki karewa, kuma ya kama shugaba Buhari ya san da gaskiyar lamarin.  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Akwai masu zagon kasa wajen yaki da boko haram kuma ba a son Buhari ya sani - Zulum Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama