A shirye muke mu yi tafiya tare da mawallafa labarai ta yanar gizo a zamanace - Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana kudurin Gwamnatin jihar Kebbi wajen jawo masu watsa labarai ta hanyar kafofin zamani na yanar gizo masu zaman kansu a jihar Kebbi domin a yi tafiya tare da su a Gwamnatance ta hanyar basu kulawa ingantacce, yayinda su kuma za su yi aiki tukuru domin bayyanar da fasaharsu ta sadarwa domin ganin Gwamnati da al'umman jihar Kebbi sun sami gamsuwa da nassara a labarance.

Gwamna Bagudu ya yi wannan jawabi ne lokacin wanio taro na tattaunawa da Gwamnatin jihar Kebbi ta dauki nauyi kuma aka gudanar a dakin taro na shugaban kasa da ke garin Birnin kebbi ranar Talata.

Yayin da yake amsa tambaya da wani masani kuma kwararre ta fannin ingizon wayarr salula, Mawallafi,  kuma shahararren  mai shiga silasilar ingizon aikatau na na'urori da baya cutarwa (Ethical Hacker) Mal. Isyaku Garba Zuru ya yi masa.

Gwamna Bagudu ya ce " A shirye Gwamnati take domin ganin ta albarkaci duk wani tsari mai amfani da masu watsa labarai ta yanar gizo za su kawo. Yanzu ya rage gareku a matsayinku na kwararru a wannan fanni ku tsara kanku kuma ku gabatar mana ta jaddawalin shawarwarin ababen da kuke ganin ya kamata Gwamnati ta yi, mu kuma za mu al;barkaci bukatar domin ci gaban jihar Kebbi".

Kalli bidiyo jawabin Gwamna Bagudu:
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN