Sirri da kuma magani guda 5 da Gwanda ke yi a jikin dan adam

Ba haka kawai bane Ubangiji ke yi kayan marmari, tabbas akwai wasu manyan baiwa da ke tattare da su. Gwanda babban abun marmari ne mai tarin albarkatu. Gudumawar da gwanda ke bai wa lafiyar jikin dan Adam na da tarin yawa.

Tana dauke da sinadaran magani sanannu da jama'a da yawa a fadin duniya suka sani. Ilimi ya nuna cewa gwanda tana dauke da sinadaran Vitamin A, C, E da K. Tana kunshe da Magnesium, potassium, niacin, carotene, protein, fiber da kuma papain, wanda ke maganin mura da kashe wasu kwayoyin cuta a jiki.

Za ka sha matukar mamaki idan ka gano amfanin gwanda. Abin mamakin shine, bincike ya nuna cewa hatta 'ya'yanta na matukar taimakawa fatar dan Adam tare da sany ata walkiya.

Ga wasu amfanin gwanda 5 ga dan Adam.

1. Tana kara hasken fata Sanannen abu ne cewa gwanda tana goge fata tare da taimakawa wurin cire dattinta. Kunsar sinadarin Vitamin C da tayi yasa take bada kariya wurin lalacewar fata.
2. Tana hana bayyanar alamun tsufa ko shekaru Gwanda tana saka fata ta yi laushi da santsi. Tana iya bada wannan amfanin ne sakamakon sinadaran Vitamin da ke cikinta. Akwai sinadarin alpha hydroxy acid wanda ke hana bayyanar alamun shekaru ta hanyar kashe matattun 'ya'yan halitta. Vitamin C da E suna boye shekaru tare da rage tsufa.
3. Tana yakar fimfus da tabbansu Bincike ya nuna cewa sinadarin Papain da ke kunshe a gwanda na goge fata. Hakan yasa kofofin fata da suke toshe ke budewa. Hakazalika, matacciyar fata na fita da taimakon sinadarin hydroxy acid. Hakan na hana fimfus da tabbai.
4. Gwanda tana hana bushewar fata A nan, 'ya'yan gwanda na bada mamaki. Ana amfani da su ga fata mai laushi ko mai tauri. Sakamakon sinadaran Vitamin da Minerals da ta kunsa, tana hana bushewar fatar mai amfani da ita.
5. Gwanda na maganin tattarewar fata sakamakon tsufa da kuma tsagewar kafa yayin sanyi Bincike ya nuna cewa gwanda na hana bayyanar tattarewar fata sakamakon tsufa sannan tana maganin tsagewar kafa yayin sanyi. Tun a farko an san tana kunshe da sinadaran Vitamin C, wannan kadai yana iya yakar duk wani abu da ke lalata fata.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN