Jami'an tsaron hadin guiwa na kasa da kasa (MNJTF) sun karba mayakan ta'addancin Boko Haram 47 da suka mika wuya ga dakarun a yankin tafkin Chadi.
Shugaban fannin yada labarai na MNJTF da ke N'Djamena a Chad, Kanal Timothy Antigha, a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a, ya ce 'yan ta'addan sun mika kansu tare da iyalansu ga jami'an tsaron hadin guiwar.
Antigha ya ce rikicin shugabanci da ya barke a tsakanin manyan 'yan ta'addan, rikicin kabilanci da rashin samun gamsasshen wanda zai shugabancesu na daga cikin abubuwan da yasa suka mika wuya.
Ya ce daya daga cikin 'yan kungiyar da ya tabbatar ya taka rawar gani a harin Banki, Fotokol, Gamborou Ngala, New Matte, Chikun Gudu da sauransu, ya bayyana rashin jin dadin sa da rashin ci gaban jihadin.
Antigua ya bayyana cewa tubabbun 'yan ta'addan sun ce sun mika wuya ne saboda sanya son abin duniya da aka yi yayin neman shugabancin kungiyar.
"Sun sanar da mu cewa gwamnati na mana karya tare da cutarmu, amma har yanzu ban ga banbanci tsakanin Shekau da wadanda yake kushewa ba.
"Akwai yuwuwar ya fi su rashin imani. Na fi son nan saboda tun bayan mika wuya da muka yi ana ciyar da mu tare da kula da mu," daya daga cikinsu yace.
Antigha ya kara da cewa, daya daga cikin wadanda suka mika wuyan ya yi ikirarin cewa an batar da shi ne har ya je yana kashe mutane ba tare da laifin komai ba.
Ya ce 'yan ta'addan sun kara da cewa akwai banbancin kabila a tsakanin 'yan Boko Haram da ISWAP.
Ya ce, "Idan kai baka iya wani yare ba, toh ba za a nada ka kwamanda ba kuma za a iya mayar da kai mai gadi a daji ko kuma ba za ka iya zuwa karbar haraji ba.
"Wannan halayyar ta kabilanci ta sa wasu daga cikinmu suke ganin ba a yarda da su ba kuma ba a basu shugabanci."
Kakakin ya kara da cewa, wata mace daga cikin tubabbun ta bayyana yadda ake matukar cin zarafin mata a sansanin kuma ta yi addu'ar kada Allah ya nuna wa wata mace halin da ta shiga.
Ta ce, "wadannan mutanen babu Allah a zuciyarsu. Ba zai yuwu su dinga cewa abinda suke yi a duniyar nan saboda Allah suke yi ba."
Antigah ya ce MNJTF tana ci gaba da lura da mayakan ta'addancin Boko Haram da ISWAP wadanda sun hada 'yan kasashe ne da aka kafa da wasu akidu.
"Hukumar na amfani da abinda tubabbun 'yan ta'addan suka sanar da kansu.
"MNJTF na ci gaba da kira ga sauran 'yan ta'addan da aka batar da miyagun akidu kuma suke daji da su fito.
"Hakazalika, tana kira ga yankuna da su karba tubabbun 'yan ta'addan bayan sun sauya hali. Duk da irin laifukan da suka aikata a baya.
"MNJTF ta aminta da cewa wannan karamcin zai taka rawar gani wurin tabbatar da cewa an yaki ta'addanci tare da gina zaman lafiya a yankin tafkin Chadi," yace.
Source: Legit
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/