• Labaran yau


  Karamin soja ya budewa babban soja wuta a jihar Borno

  Wani karamin soja da ake zargin ya na fama da ciwon matsananciyar damuwa (depression) ya budewa wani babban soja wuta a ranar Laraba. Babban sojan ya mutu nan take.
  Jaridar The Nation ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a jihar Borno kuma har yanzu rundunar soji ba ta saki bayanan sojan da aka harbe ba.
  Shi kansa sojan da ya yi kisan ba a bayyana sunansa ba bayan sanin cewa karamin soja ne da ke aiki da bataliya ta 202 a karkashin rundunar soji ta 21 da ke Bama a jihar Borno.
  Kanal Sagir Musa, mukaddashin jami'in hulda da jama'a na rundunar soji, ya ce; "wani karamin soji da ke tare da bataliya ta 202 a runduna ta 21 da ke Bama a jihar Borno ya tubure da misalin da 10:30 na ranar 29 ga watan Yuli, 2020, tare da budewa babban soja wuta, lamarin da ya zama silar mutuwarsa.
  "Ya bude ma sa wuta ne a lokacin da ya zo wurinsa shi kuma ya na magana a waya. An kama karamin sojan tare da fara gudanar da bincike. Yanzu al'amura sun koma daidai."

  Source: Legit


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karamin soja ya budewa babban soja wuta a jihar Borno Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama