Janar Adeniyi zai gurfana a Kotun soji don ya ce soji basu da wadatattun kayan yaki da BH

Tsohon Kwaamandan askarawan sojin Najeriya da ke karkashin Operation Lafiya Dole da ke gumurzu da boko haram a arewa maso gabas na Najeriya Janar Olusegun Adeniyi, zai fuskanci Kotun soji bayan ya yi koken cewa rundunar na fama da karanci albarussai domin tunkarar yan ta'addan.

Olusegun Adeniyi, yana cikin soji 886 da hukumar soji za ta canja ma wajen aiki ranar Talata 14 ga watan Juli, haka zalika an mayar da shi Shelkwatan sojin Najeria a Abuja domin fuskantar Kotun sojin a cewa jaridar Premium Times.

Major-General Olusegun Adeniyi ya bayyana a wani bidiyo da ya yi tashe a shafukaan intanet inda yake bayani kan rashin wadataccen kayan fada da boko haram wanda ya ce sakamakon haka sojin Najeriya ta yi asarar soji da dama.

Wata majiya ta shaiada wa jaridar Premium Ti,mes cewa hukumar soji tana jiran rudani da wannan bidiyo ya jawo a shafukan intanet ya lafa kafin a tuhumi Janar Adeniyi, wanda ake tsammanin zai gurfana a Kotun soji da ake kira "Courtmarshal" ranar 20 ga watan Juli 2020.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN