Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya kwashe wasu komatsansa daga shelkwatan hukumar a cewar rahotun Jaridar Tribune Online.
Rahotun ya ce Magu ya umarci wasu jami'ansa su kwashe wasu daga cikin komatsansa daga ofishinsa a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa fadar shugaban kasa ranar Talata domin ci gaba da fuskantar binciken Kwamiti.
Rahotun ya kuma yi bayanin yadda masu taimaka masa a hukumar suka shigo shelkwatan hukumar da motoci biyu domin kwashe komatsansa kuma ana zaton za su sake dawowa ranar Laraba domin su karasa kwashe sauran komatsansa.
Ibrahim Magu na fuskantar tuhume tuhume 22 a gaban wani Kwamiti da ke zamansa a fadar shugaban kasa.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari