Cikin gaba da Fatiha da Aisha yar Gesse 1 ta dauka a Birnin kebbi zance ya kai Kotu

Wata yarinya mai suna Aisha Salihu, ta gaya wa Kotu cewa ta sami juna biyu ne sakamakon hulda na kwanciya da ta yi da wasu maza guda biyu, kuma sakamakon haka ta dauki cikin gaba da Fatiha a garin Birnin kebbi.

Aisha wacce ke zaune a unguwar Gesse 1 a Birnin kebbi ta shaida wa Kotu cewa mazan guda biyu, su ne suka dura mata ciki bayan sun yi ta aikata jima'i da ita lokaci da dama.

Ta ce " Dakinsa na unguwar  Tsohon Mayanka, a nan muke kwana tare da shi a kan Katifa daya. Ya sha yin jima'i da ni ba tare da yin amfani da Kwararon roba ba (Condom) hatta kudin da na samo yakan amfana da su. Domin nikan yi amfani da kudin domin in ciyar da kaina sau da yawa kuma ina sayo abinci da kudina kuma shi ma ya ci.

Aisha Salihu ta bayyana wa Kotu dalla dalla yadda da sadu da mazan guda  biyu lokaci daban daban kafin ta sami juna biyu.

Tun farko dai, mai gabatar da kara na yan sanda Cpl.Faruku Muhammad, ya gabatar wa Kotu cewa wadanda ake zargi mutum biyu ne a kan laifi guda biyu da suka hada da
1 - Hulda da karamar yarinya da
2 - Aikata zina wanda ta haka ta dauki juna biyu (Ciki).
Karkashin sashe doka na 127 da 235 na Penal Code ( Ammendment 20000) wanda aka yi ma gyara a 2000.

A nasu kariya, wadanda ake zargin kuma mazauna garin Birnin kebbi, sun musanta tuhuma da ake yi masu a gaban Kotu ta hanyar bayar da bayanan yadda suka gudanar da hulda da Aisha.

ISYAKU.COM  ya  samo cew hukumar Hisbah na jihar Kebbi ce ta bankado wannan bincike wanda ya kai ga gabatar da kara a gaban babban Kotun Shari ta 2 a garin Birnin kebbi da misalin karfe 11 na safe ranar Juma'a 24 ga watan Yuni.

Alkali Mu'awuyya Shehu Birnin kebbi, ya tasa keyar wadanda ake zargi zuwa Kurkuku har zuwa ranar Laraba 29 ga watan Yuni domin ci gaba da shari'ar.

Sai dai mai gabatar da kara Cpl. Faruku, ya ce" Za mu gabatar da shaidu domin tabbatar da da'awar mu a gaban Kotu kan wadanda muka gurfanar a gabanta".


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN