Cikakken rahotun ababen da suka faru da Magu ranar Talata bayan Buhari ya kware masa baya


Ibrahim Magu: Shin shugaban EFCC zai bi sawun Lamorde, Waziri da Ribadu ne?

Ana ci gaba da ƙila-wa-ƙala game da inda shugaban hukumar da ke yaƙi masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon- ƙasa ya shiga.

A ranar Litinin ne Ibrahim Magu ya bayayana a gaban wani kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa don bincike a kan cin hanci, sakamakon wani zargin da ake yi masa.

Kuma tun daga lokacin wasu rahotanni ke cewa an kama shi amma, kakakin hukumar EFCC ya musanta, yana cewa gayyata aka yi masa.

Rashin fitowar mahukunta a Najeriya su fadi takamaimen inda Ibrahim Magu, wato muƙaddashin shugaban hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasar zagon- ƙasa, wato EFCC ya yake, ya ba da kafa ga wasu 'yan Najeriya ta yin shaci-fadi ko rade-radi game da al'amarinsa.

Tun da farko dai an ba da labarin cewa jami'an hukumar tsaro ta farin-kaya, wato DSS ne suka kama shi, amma daga bisani sun musanta, har ma hukumar EFCCn da bakinta ta ce gayyata kawai aka yi wa Mista Magu domin ya gurfana a gaban kwamitin shugaban kasa da ke gudanar da bincike a kan cin hanci.

Amma wasu na dasa ayar tambaya a kan wannan ikirarin, suna cewa da gayyata ce ta girma da arziki, da jami'an tsaro ba su yi masa daukar-amarya a gaban hedikwatar EFCCn ba.

Bayanan da ke fitowa na baya-bayan nan dai sun tabbatar wa BBC cewa Mista Magu ya kwana ne a hannun jami'an 'yan sanda masu gudanar da bincike, bayan ya kwashe sa'o'i yana amsa tambayoyi daga 'yan kwamitin shugaban kasa, wadanda aka ce za su ci gaba da yi masa kwakwa a ranar Talatar.

Ofishin ministan shari'ar Najeriya ne ya ne ya fitar da wani rahoto, wanda a ciki ya yi zargin mukaddashin shugaban hukumar EFCCn da rashin saurarom magabatansa da kuma yin rub-da-ciki ko kin fitowa ya yi bayani a kan wasu daga cikin kudi da kadarorin da hukumar ta kwata daga hannun wasu jami`an gwamnati, zargin da ya musanta.

Wasu masu yaki da cin hanci a Najeriyar na sukar hanyar da kwamitin ya bi wajen binciken Ibrahim Magu, suna cewa ba ta dace ba da darajar ofishinsa ba.

Malam Awwal Rafsanjani jami'i ne na kungiyar Transparency Internationalya ce wani laifin ma na gwamnati ne, tun da ba ta nada 'yan hukumar gudanarwar EFCCn ba, ga shi an bar mukamin shugabanta yana reto shekara da shekaru.

Duk da cewa suna musantawa, ana zargin cewa Mista Magu ya hau tsini ne sakamakon zaman-tsamar da ake yi irin ta 'yan uba tsakanin wasu da ake yi wa kallon 'yan cikin-gida a tsakanin manyan mukarraban shugaban Najeriya.

Tun da aka kafa hukumar EFCC, mutum hudu ne suka jagorance ta domin yaki da cin rashawa daga Malam Nuhu Ribadu wanda ya yanke mata cibi zuwa Ibrahim Lamurde zuwa Farida Waziri sai kuma Ibrahim Magu.

Sai dai a halin yanzu, kamar sauran magabatansa Ibrahim Magu wanda shi ne jan ragamar hukumar ta EFCC yana fuskantar kalubale tare da zargi mai karfi kan cewa shi ma ana zarginsa da cin hanci da karbar rashawa.

Hakan ya yi kama da abin da ake cewa mai farauta ya zama wanda shi ake farauta, tun da a yanzu Magu shi ke amsa tambayoyi kan rashawa ba wai shi ne ke yi wa mutane tambayoyi kan batun ba.

Magu na fuskantar kalubale kamar yadda Shugaba Buhari ya cire Ibrahim Lamorde saboda ana zarginsa da cin hanci da rashawa, zargin da ya musanta.

Kafin Lamorde, Mrs Farida Waziri ce shugabar EFCC, ita ma zargin cin hanci da rashawa ya ci kujerarta a lokacin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan. Kuma a shafin Twitter aka sanar da cire Mrs Waziri daga kujerarta.

An tsige ta ne bisa zargin tana nuna bangaranci wajen yaki da rashawa da kuma zargin cewa ta sa wa 'yan jam'iyyar PDP ido.

Bisa al'ada idan aka soma irin wannan bincike da kamar wuya shugaba ya tsira, kuma tarihi ya nuna cewa Ibrahim Magu na kan siradi.

Tun da aka bashi rikon mukamin a shekarar 2015, bai samu hawa kujerar ta dindindin ba saboda majalisar dattijai a wancan lokacin karkashin jagorancin, Bukola Saraki ta ki amincewa da nadinsa saboda zargin cewa hukumar tsaro ta DSS ta aike mata wasu bayanai na rashin gamsuwa kan Ibrahim Magu.

A yanzu kuma akwai alamun rashin jituwa tsakaninsa da ministan shari'a Abubakar Malami, lamarin da ya sa wasu ke ganin cewa da kamar wuya ya tsallake wannan siradin.

Tsohon shugaban kotun daukaka kara a Najeriya, Mai Shari'a Ayo Salami ne ke shugabantar kwamitin bincike kan zarge-zargen da ake yi wa shugaban EFCC na riko, Ibrahim Magu kuma Salami ya yi kaurin suna wajen aiki ba sani ba sabo.

Daga takun saka ne da manyan jami'an gwamnati aka cire Malam Nuhu Ribadu a zamanin mulkin Shugaba Umaru 'Yaradua.

Mrs Farida Waziri ita ma ta sauka ne bayan 'yan siyasa a mulkin Shugaba Jonathan sun zarge ta da aikata ba daidai ba - amma ta musanta zargin.

Ibrahim Lamorde kuwa ya sauka ne bayan da Shugaba Buhari ya sha alwashin bude sabon babi a yaki da rashawa.

Bayanai sun ce binciken da ake yi wa Magu na da nasaba da wata wasika da ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami ya aike wa Shugaba Buhari kan zargin shugaban na EFCC na amfani da ofishinsa ba bisa ka'ida ba.

Masu sharhi dai na ganin da wuya Magu ya tsallake domin ko a yanzu ana iya cewa yana bankwana da wannan kujera, ganin bisa ka'ida ba a soma yi wa mutum irin wannan bincike yana kan mukami.

Ita ma wata majiya mai karfi daga fadar gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa BBC cewa, Ibrahim Magu kusan ana iya cewa ya yi adabo da wannan kujera domin fuskantar sauran tuhume-tuhume.

A wannan Talatar ake saran ci gaba da sauraran bahasi daga Magu, kuma mai yiwuwa ne ba za a dau lokacin wurin sanar da matsayar da aka cimma ba

Ibrahim Magu: Fadar shugaban Najeriya ta dakatar da shugaban EFCC

Fadar shugaban kasa ta dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki ta Najeriya EFCC.

Wata majiya mai karfi da ta bukaci a sakaya ta daga Fadar shugaban Najeriya ce ta tabbatar wa da BBC Hausa hakan a ranar Talata.

A ranar Litinin ne Ibrahim Magu ya bayyana a gaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na aikata ba daidai ba

Kwamitin - karkashin jagorancin tsohon mai shari'a Ayo Salami - ya gayyaci Mr Magu ne domin jin ta bakinsa kan abubuwan da suka shafi jagorancinsa a hukumar ta EFCC.

Wasu majiyoyi a Najeriya sun tabbatar cewa Magu ya kwana a tsare a hannun jami'an tsaro saboda ba a kammala binciken da aka soma ba a ranar Litinin.

A ranar ta Litinin ne rahotanni suka nuna cewa jami'an tsaron DSS a kasar sun kama Ibrahim Magu.

Sai dai wata sanarwa da DSS da kuma EFCC suka fitar daban-daban sun ce ba kama Mr Magu ta yi ba.

EFCC ta ce ya amsa gayyatar jami'an tsaro ne kawai, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter.

Shi ma kakakin DSS Peter Afunanya ya ce: "DSS tana so ta shaida wa al'umma cewa ba ta kama Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban EFCC ba, kamar yadda wasu kafafen watsa labarai suka bayar da rahoto."

Tun da aka bayar da labarin kama shi har yanzu wannan lokaci ba a ga Mr Magu ba.

Rashin fitowar mahukunta a Najeriya su fadi takamammen inda yake, ya ba da kafa ga wasu `yan Najeriya ta yin shaci-fadi ko rade-radi game da al'amarinsa.

Bayanan da ke fitowa na baya-bayan nan dai sun tabbatar wa BBC cewa Mr Magu ya kwana ne a hannun jami'an 'yan sanda masu gudanar da bincike, bayan ya kwashe sa'o'i yana amsa tambayoyi daga `yan kwamitin shugaban kasa, wadanda aka ce za su ci gaba da yi masa kwakwa yau din nan.

10 daga cikin tuhume tuhume 22 da aka yi wa Ibrahim Magu

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa fadar shugaban kasa ta dakatad da Ibrahim Magu matsayin mukaddashin shugaban hukumar EFCC, BBC ta ruwaito. Mun kawo muku rahoton cewa mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, na tsare a ofishin yan sanda kuma a nan ya kwana.

Da misalin karfe 10:15 na dare bayan kwamitin binciken fadar shugaban ta kammala yiwa Ibrahim Magu tambayoyi, jami'an yan sandan sun yi awon gaba da shi ne daga fadar shugaban kasa. Tuni Majiya ta bayyanawa The Nation cewa da wuya Magu ya tsira daga dakatad da shi.

"Hanashi komawa ofishinsa alama ce dake nuna cewa za'a dakatad da shi. "Ya bayyana karara cewa fadar shugaban kasa ta kammala shirin neman sabon wanda zai maye kujerar." Cewar Majiyar.

Ga jerin tuhume-tuhume 10 cikin 22 da ake yiwa Ibrahim Magu

1. Tufka da warwara wajen lissafin kudaden da EFCC ta kwato hannun barayin gwamnati
2. Ikirarin cewa N539bn aka kwato maimakon N504bn
3. Rashin biyayya ga ofishin Antoni Janar na tarayya
4. Rashin gabatar da isassun hujjoji domin dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya
5. Bata lokaci wajen binciken kamfanin P&ID wanda ahakan ya kai ga rikicin da ake a Kotu yanzu
6. Kin bin umurnin kotu na sakin asusun wani tsohon diraktan banki kimanin N7bn
7. Bata lokaci wajen daukan mataki kan jiragen ruwa biyu da hukumar Sojin ruwa ta kwace
8. Fifita wasu jami'an EFCC kan wasu wadanda akafi sani da 'Magu Boys'
9. Kai wasu Alkalai kara wajen shugabanninsu ba tare da sanar da Antoni Janar ba
10. Sayar da dukiyoyin sata ga yan'wansa, abokan arziki da abokan aiki

A ranar Litinin, an gayyace Ibrahim Magu, fadar shugaban kasa domin amsa tambayoyi da wasu tuhume-tuhume da ake yi masa kimanin 22.

LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPost a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN