Bata gari sun kashe wani basarake a Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi

Allah ya yi wa Sarkin Bajida rasuwa ranar Talata bayan wasu bata gari sun farmake shi a kan hayarsa ta komawa Bajida daga Zuru ranar Talata 7 ga watan Yuli..

Majiyarmu ta tabbata mana cewa Sarkin Bajida Alhaji Musa Muhammed, dan shekar hamsin, ya rasa ransa ne da karfe shida saura kwata na yamma, yayin da yake tuka motarsa shi kadai daga Zuru zuwa Bajida, bata garin suka tare shi a wani kauye da ake kira Dan Mangoro kuma suka kashe shi.

Kauyen Dan Mangoro yana karkashin Sarautar Bajida da ke karamar hukumar Fakai a Masarautar Zuru na kudancin jihar Kebbi.

Mun samo cewa Kakakin hukumar yansandan jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar ya ce "Rundunar yansandan jihar Kebbi ta dukufa ne wajen ganin an kama wadanda suka aikata wannan laifi, domin tana bincike kan lamari".

Hakazalika wata majiya da bata son a ambaci sunanta, ta shaida mana cewa " Rundunar yansandan jihar Kebbi ta sa zababbun zaratan yansanda masu binciken kwakwaf domin gudanar da bincike tare da ganin am kama wadanda suka yi wannan danyen aiki".

Manyan mutane daga kowane bangare na rayuwa a ciki da wajen jihar Kebbi, da daruruwan jama'a na ci gaba da kai gaisuwa ga yan uwan basaraken tare da yi ma iyalansa fatar gafara da rahamar Allah, da kuma aduu'an neman Allah ya tona asirin wadanda suka kashe shi.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post