‘Yan sanda sun kama ‘Yan KAROTA da suka yi wa wani dukan kawo wuka

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kame  wasu jami’an Hukumar Kula da Ababen Hawa (KAROTA) na jihar, bisa  zarginsu da lakada wa wani magidanci duka har suka karya shi.

Fitaccen dan jarida a Kano Salis Zango ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa  kawo Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar CP Habu Sani  ya umarci a mayar da binciken zuwa  hedikwatar rundunar da ke Bompai.

Ya ce wata majiyar ‘yan sanda ta ce kame ‘yan Karotan  ya fusata Hukumarsu har ta janye jami’anta daga hanyoyin jihar inda a baya suka saba gudanar da ayyukansu.

Sai dai Kakakin KAROTA, ya musanta hakan, inda ya ce  babu tabbacin cewar ‘yan karota ne suka aikata wannan mummunan aiki, sai dai bincike zai bayyana gaskiyar lamarin.

A nasa bangaren Kakakin Rundunar’Yan Sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Kiywa  ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ana kan bincike a kai.

A ‘yan kwanakin nan ana samun tangarda a yanayin tafiyar da aikin jami’an KAROTA a Kano, domin ko a makon jiya an zargi  wani jami’in Hukumar da galabaitar da wani matashi ta hanyar jona wa wata na’ura mai kashe jiki.

Da yawan mutane na kalubalantar hukumar ta KAROTA bisa yadda take wuce makadi da rawa a ayyukanta.

Wasumasana sharia na cewa hatta cin tarar kudi da karota ke yi a yanzu ya saba da doka, domin kotu ce kadai ke da ikon cin tarar mutane idan sun yi laifi,  kuma kotuna suna hutun COVID-19, amma duk da hakan jami’an na ci gaba da cin tarar mutane.

Haka ma maganar dokar hana goyon babur da KAROTA ta ayyana shi ma masana sharia na cewa tamkar shiga sharo ne ba shanu.

Rahotun Jaridar Aminiya


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN