An kama Badmus ranar Alhamis 11 ga watan Yuni, bayan makwabciyarsa ta shigar da kara a kansa a ofishin yansanda da ke Owode Egbado.
Mahaifiyar yarinyar ta shaida wa yansanda cewa ta gan jini yana fitowa daga al'aurar diyarta mai shekara 3, bayan ta tambayeta ko me ya faru da ita sai ta ce Badmus ne ya kai ta dakinsa ya yi lalata da ita.
Sakamakon haka, DPO na ofishin yansanda na Owode Egbado, SP Olabisi Elebutte ta jagoranci masu bincike suka kama Badmus nan take.
Kakakin hukumar yansanda na jihar Osun DSP Abimbola Oyeleye ya tabbatar da faruwarv lamarin., yayin da aka garzaya zuwa Asibitin Idiroko da yarinyar domin samun kulawan Likita.
Haka zalika bayanai sun ce Kwamishinan yansandan jihar Osun ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da ganin cewa an hukunta mai laifin.
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari