Hotunan tarihi: Janar Abdulsalam Abubakar ya cika shekara 78 a Duniya

Ranar 13 ga watan Yuni, tsohon shugabn kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya cika shekara 78 a Duniya.

An haifi Janar Abubakar ranar 13 ga watan Yuni 1942. Ya zama shugaban kasa daga 1998 zuwa 1999, ya kuma rike mukamin shugaban askarawan Najeriya daga 1993 zuwa 1998. Ya zama shugaban kasa bayan rasuwar shagaban kasa Janar Sani Abacha.
A lokacin shugabancinsa, an yi wa tsarin mulki na 1979 kwaskwarima, kuma aka wanzar da jam'iyyun siyasa da dama.

Ya mika mulkin Najeriya daga shugabancin soja zuwa na farar hula ga shugaba Olusegun Obasanjo a ranar 29 ga watan Mayu 1999.

Yanzu shi ne shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa watau National Peace Committee.
.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN