Yansandan jihar Anambra sun kama wani mahaifi dan shekara 34 mai suna Ifeanyi Apusiobi daga garin Azu Ogbunike a karamar hukumar Oyi bayan ya kwantare diyansa biyu da tabarya har lahira.
Wannan mutum ya sami yayansa masu suna Chinecherem Apusiobi mai shekara 7 da kaninsa Obinna Apusiobi mai shekara 5 suna barci sai ya dinga dukansu da tabarya har suka mutu.
Daga bisani kuma ya yi wa mahaifinsa mai shekara 72 manyan raunuka a kai.
Yansanda sun kai gawakin yaran Asibiti inda Likita ya tabbatar da mutuwarsu.
Yansandan sashen CID suna gudanar da binciken sirri kan lamari.
AGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari