• Labaran yau


  Duba yara yan shekara 7 da 5 da mahaifinsu ya kashe ta hanyar duka da tabarya yayin da suke barci

  Yansandan jihar Anambra sun kama wani mahaifi dan shekara 34 mai suna Ifeanyi Apusiobi daga garin Azu Ogbunike a karamar hukumar Oyi bayan ya kwantare diyansa biyu da tabarya har lahira.


  Wannan mutum ya sami yayansa masu suna Chinecherem Apusiobi mai shekara 7 da kaninsa Obinna Apusiobi mai shekara 5 suna barci sai ya dinga dukansu da tabarya har suka mutu. 


  Daga bisani kuma ya yi wa mahaifinsa mai shekara 72 manyan raunuka a kai.


  Yansanda sun kai gawakin yaran Asibiti inda Likita ya tabbatar da mutuwarsu.


  Yansandan sashen CID suna gudanar da binciken sirri kan lamari.  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Duba yara yan shekara 7 da 5 da mahaifinsu ya kashe ta hanyar duka da tabarya yayin da suke barci Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama