Gwamnatin tarayya ta yi asarar N1.01tn a kudin shiga sakamakon cutar Korona

Faduwa a kudin shigar, kamar yadda wata takarda da ta bayyana daga the whistler.ng wacce tace ta fito daga ofishin kasafin tarayya ne, an gano cewa hakan ta faru ne saboda faduwar da raguwar kudin shiga da ke shigewa asusun tarayya.

Annobar ta kara da kawo faduwar farashin danyen man fetur a fadin duniya. Barkewar muguwar cutar ta korona ya janyo dokar hana walwala a jihohi daban-daban na fadin kasar nan, ci gaban da ya gurgunta al'amuran tattalin arziki.

A misali, daga cikin N1.96 tiriliyan da gwamnatin tarayya ta yi tsammanin samu na kudin shiga a watanni ukun farkon shekarar nan, ta samu N950.55 biliyan. Idan aka dogara da kiyasin kudin shigar, faduwar da asarar N1.01 tiriliyan na nuna asarar kashi 52 na kudin shiga.

Game da dukkan kudin shiga, annobar ta taka rawar gani wurin kawo asarar kashi 30 daga N659.4 da aka yi kiyasin samu. Kudin shigar da aka samu a cikin watanni uku a bangaren man fetur shine N464.03 biliyan. Hakazalika, an ga illar annobar a bangaren iskar gas da aka yi kiyasin samun N31.07 biliyan. A wani labari na daban,

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan ya ce idan annobar COVID-19 ta ci gaba, a kalla 'yan Najeriya miliyan 20 ne za su rasa aikinsu. Lawan ya kara da cewa, siyasar kasa da kasa ke hana Najeriya samar da makaman zamani don amfanin rundunar soji wajen fatattakar rashin tsaro.

A yayin jawabi ga manema labarai a garin Abuja yayin shirye-shiryen bikin zagayowar shekara na majalisar, Lawan ya ce duk lokacin da Najeriya ta bukaci siyan makamai daga kasashen ketare, ana daukar tsawon lokaci kafin aminta.

Rahotun Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN