Rahotanni daga babban bornin tarayya, Abuja na cewa babbar kotun
gwamnatin tarayya dake Abuja ta ci tarar hukukar ‘yansanda Naira Miliyan
15 kan kisan ‘yan Shi’a 3 inda ta bukaci a biya ‘yan shi’ar kudin a
matsayin diyya.
Mai shari’a Taiwo Taiwo ne ya yanke wannan hukunci a yau,
Litinin inda kuma ya bukaci babban Asibitin Abuja da ya baiwa ‘yan
Shi’ar gawar mamatan.
Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya bayyana cewa a biya kowane daga cikin masu karar su 3 diyyar Miliyan 5 saboda kashe musu ‘yan uwa.
Kamfanin
dillancin Labaran Najeriya,NAN ya ruwaito cewa saidai Mai shari’a Taiwo
ya ki amincewa da bukatar ‘yan Shi’ar kan tursasa Hukumar ‘yansandan ta
basu hakuri ta hanyar bugawa a jarida saboda kisan.
Wanda aka kashe din
sune, Sulaiman Shehu, Mahdi Musa, Bilyaminu Abubakar Faska, da Askari
Hassan. Saidai har aka yi Shari’ar aka gama hukumar ‘yansadan Najeriya
bata aike da wakili ba ko kuma lauya.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari