Type Here to Get Search Results !

Yunkurin binne gawar surukin Ganduje a Masallaci ya tayar da kura tsakanin Malamai da iyalan mamacin

Wasu al’ummar Musulmi sun yi gargadi a kan shirin iyalan tsohon gwamnan jihar Oyo Marigaya Sanata Abiola Ajimobi, na binne shi a cikin masallaci.

Tun da fari dai kakakin mamacin, Bolaji Tunji ya sanar cewa za a binne shi a babban masallacinsa da ke Oke-Ado a garin Ibadan, babban birnin jihar a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuni da karfe 12.00 na rana.

Wasu al’ummar Musulmi sun bayyana yunkurin a matsayin haramtacce a Musulunci, inda suka ce hakan ka iya wofantar da masallacin.

Da yake tsokaci bisa lamarin, wani malamin addinin Musulunci a yankin, Ustaz Ibrahim Akinola cewa ya yi, Manzon Allah Sallal Lahu alaihi wa sallama ya hana binne mamata a masallaci, ya hana a gina masallaci a kan kabari, ya kuma la’anci wanda ya yi hakan.

“Manzon Allah ya ce yin haka aiki ne na Yahudu da Nasara.

“Gina masallaci a kan kaburbura ko binne mamata a cikin masallaci, hakan zai sanya mutane yi wa Allah tarayya da waninSa a wajen bauta.

“Mutane za su rika riyawa a zukatansu cewa wadanda aka binne a masallaci suna da wata daraja ta musamman da za ta amfanesu ko kuma ta kare su daga wani abu.

“Wannan tamkar yi wa Allah Madaukakin Sarki abokan tarayya ne”, inji shi.

Ustaz Akinola ya ce kamata ya yi al’ummar Musulmi su kwana da sanin hadarin binne mamata a cikin masallatai, su kuma sani cewa ana gina masallaci ne bisa doron kadaita Allah tare da tsoronSa.

Haka shi ma wani malamin a jihar Oyo, Shaikh Abdallah Qasim, ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa “Al’ummar Musulmin Jihar Oyo da na garin Ibadan ku farka daga barcin da kuke yi .

“Don Allah kada ku binne Sanata Ajumobi a masallaci.

“Kada ku kori Musulmi masallata daga masallacin” kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 27 ga watan Yuni.

Tsohon Gwamnan jihar Oyo Sanata Ishaq Abiola Ajimobi, jigo ne a jam’iyyar APC kana suriki ga Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, kamar yanda Aminiya ta ruwaito.

An dai yi jana’izar marigayin a jiya, Lahadi inda aka binneshi a wani gidanshi.

Hutudole



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN