Yan kabilar Igbo sun rufe shagunansu a manyan wuraren sana'a da kasuwanni a fadin jihar Cross River ranar Litinin 22 ga watan Yuni.
Wuraren da lamarin ya fi yin kamari sun hada da shahararrun wuraren sana'a da mafi yawa yan kabilar Igbo ne ke da shaguna sun hada da Watt, Etim Edim da kasuwar Marian a birnin Calabar,
Yan kabilar Igbo sun dauki wannan mataki ne domin abin da suka alakanta da yawan sace yan kasuwa tare da jama'ar kabilar Igbo domin karban kudin fansa da wasu bata gari ke yi a fadin jihar.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari