• Labaran yau


  An sake gano wata cuta da ka iya zama annobar duniya a China

  Masana kimiyya sun sake gano wata sabuwar cutar mura a China da ke da yiwuwar zama annobar duniya.

  Ta bayyana ne a baya-bayan nan, kuma aladu ne ke ɗauke da ita amma mutane suna iya kamuwa a cewar masanan.

  Masu binciken sun damu da cewa cutar tana iya ƙara rikiɗa ta yadda za ta ci gaba da yaɗuwa daga wannan mutum zuwa wancan, har ma ta haddasa annoba a faɗin duniya. 

  Ko da yake dai, ba matsala ce ta gaggawa ba, amma dai sun ce tana da “dukkan alamomi” na zama mai matuƙar sassauyawa don shafar mutane dalilin da ke wajabta buƙatar yin bibiya ta ƙut-da-ƙut.

  Masanan sun ce sabuwar cuta ce, kuma ba lallai ne garkuwar jikin mutane ta iya kare su daga ƙwayar cutar ta bairas ba.

  Ƙwararrun sun rubuta a mujallar Proceedings of the National Academy of Sciences cewa kamata ya yi cikin hanzari a ɓullo da matakan taƙaita yaɗuwar ƙwayar cutar a jikin aladu kuma a riƙa matuƙar bibiyar ma’aikatan da ke aiki a masana’antun da ke harkar sarrafa naman aladu.

  Hutudole


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An sake gano wata cuta da ka iya zama annobar duniya a China Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama