An fara shari'ar wasu soji hudu da ake zargi da kashe wani bawan Allah mai suna Benon Nsimenta, mai karanta labarai.
Wani babban hafsan soji na kasar Uganda, Brig. Richard Karemire, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa sojojin sun gurfana ne a Kotun soji na sashen Mountains Division Court karkashin jagorancin Lt Col Felix Nyero da ke garin Karusandara a Kasese.
Sojojin da ke fuskntar Kotun sun hada da Abraham Lokwap, Joel Atim, Talent Akampulira da Jackson Nyero.
Ana zargin sojojin ne da kashe Benon Nsimenta ne yayin da yake tuka Keke tare da matarsa Allen a garin Karungibati da ke kan hanyar Hima-Kasese.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari