An damke korarren dansanda da ya kafa shinge yana karbar na goro a hanya - Hoto

Yansandan jihar Niger sun damke wani korarren dansanda mai suna Usman Yohanna.

A wata sanarwa da Kakakin yansandan jihar Niger ya fitar ranar shida ga watan Yuni, Wasiu Abiodun ya ce, masu bincike na yansanda karkashin jagorancin DPO na rundunar yansanda na Gawu Babangida suka ci karo da shinge da korarren dansandan tare da wasu mutane suka sa a kan hanyar Boyi Sarkin Daku.

Shi dai korarren dansandan yana sanye da tufafin mai mukamin Safeto na yansanda a lokacin da aka kama shi, sauran wadanda yake tare da su a lokacin sun ranta a na kare bayan ganin tawagar DPO.

A lokacin da yake fuskantar bincike, korarren dansandan ya ce shi Safeto ne a sashen SARS a Abuja. Daga bisani bincike ya bankado cewa shi korarren dansanda ne a ofishin yansanda da ke Sabon Tasha a jihar Kaduna, wanda aka kora da mukamin Sajen tun watan Fabrairu na 2019.


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

0/Post a Comment/Comments

Rubuta ra ayin ka

Previous Post Next Post