Ministan shari'a Abubakar Malami ya taba rayuwar talakawan jihar Kebbi da kyautar bazata

 
Ministan shari kuma babban Jojin Najeriya Abubakar Malami (SAN) ya taba rayuwar jama'ar jihar Kebbi ta hanyar bayar da kyautar dubu dubatan buhun shinkafa ga Talakawa a lungu da sakon na jihar a cikin watan Ramadan.

Wannan tallafi ya zo ne a daidai lokaci da jama'a ke dakon ganin fitowar taimako daga masu hannu da shiuni, yan siyasa ko manyan ma'aikatan gwamnatin jihar Kebbi.

Sai dai bincike da muka gudanar ya nuna taimako da Abubakar Malami ya bayar ga talakawan jihar Kebbi a cikin watan Ramadan, ya zarce wanda sauran yan siyasa suka bayar ga al'umman jihar kawo yanzu.

Haka ya jawo wa Minista Abubakar Malami kwarjini tare da karsashi a idanun talakawa, musamman wadanda wannan tallafi ya ratsa su, ko ya shafi yan'uwa , ko makwabtansu.

Tuni taimakon shinkafan ya kai ga wasu talakawa kuma kwamitin raba shinkafa da kayan tallafi na ci gaba da gudanar da aikin rabon kayakin domin isa ga talakawa a lungu da sako na jihar Kebbi.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post