Domin an hana shi shan tabar wiwi sojin ruwa mai korona ya tsere daga wajen killacewa

Wani sojin ruwa mai suna SM Ahmadu ya tsere daga wajen da ake killace masu cutar Korona a Oghara na jihar Delta ranar 9 ga watan Mayu.

Rahotanni da muka samu sun ce Ahmadu ya yi wa Likitoci barazana da wuka Jacknife na soji kafin ya samu ya tsere daga wajen da aka killace shi tare da sauran masu Korona.

Wani ganau ba jiyau ba ya ce Ahmadu ya dauki matakin tserewa ne bayan an hana shi shan tabar wiwi a lokacin da yake killace

Mai ba Gwamnan jihar Delta shawarra  Ehiedu Anagwu, ya ce Gwamna Ifeanyi Okowa ya yi karar sojin wajen mahukuntan sojin ruwa, ya kuma bayar da umarni a nemo Ahmadu duk inda ya shiga a cikin jihar Delta.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari