Ministan shari'a Abubakar Malami ya aika muhimmin sako ga Musulmin Najeriya

Ministan shari'a kuma babban Attoni janar na Najeria Abubakar Malami (SAN) ya aike sakon taya murnar Sallar Idi ga Musulmin Najeriya.

A wani sako da ya aika ta kafar sadarwar zamani, Malami ya ce "Amadadin Iyalina da ni kaina, ina taya Musulmi murnar Sallar Idi, kuma ina kira gareku ku bi dokokin da mahukunta suka gindaya domin kare yaduwar cutar Korona a Najeriya".

Idan baku manta ba, Abubakar Malami ya bayar da taimakon bazata na kayan abinci da suka hada da dubu dubatan buhuhuwan shinkafa da sauran su ga jama'an jihar Kebbi a cikin watan Ramadan.

Lamari da ya haifar da farin ciki tare da samun gamsuwa daga talakawa, kasancewa kayakin abincin sun zo ne a daidai lokacin da jama'a ke bukata.

A hannu daya kuwa, bincike  da muka gudanar, ya nuna cewa taimakon kayan abinci da Malami ya bayar a jihar Kebbi a watan Ramadan, ya zarce yawan taimako da sauran mutane suka ba jama'a. Lamari da ya kara haska martaba da kwarjininsa a idanun talakawan jihar Kebbi.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN