• Labaran yau


  Kotun koli ta warware daurin Orji Uzo Kalu, ta sake shi daga Kurkuku har ya isa gidansa

  Rahotun Legit Hausa

  Orji Uzor Kano, Sanata mai ci da aka tura kurkuku kan laifin almundahanan kudin jiharsa ya shaki iskar yanci yayinda aka sakeshi daga gidan yari. Kalu, wanda tsohon gwamnan jihar Abiya ya samu fitowa daga gidan gyara halin dake Kuje, Abuja da safiyar Juma'a, Premium Times ta samu rahoto.

  A yanzu haka, an garzaya da shi gidansa dake cikin fadar shugaban kasa a titin Queen Amina, majiyan sun tabbatar. Majiyoyin sun bukaci a sakaye sunayensu saboda suna kusa da Orji Kalu kuma ba da izininsa suka fadawa yan jarida an sakeshi ba.

  An saki Mista Kalu ne yan mintuna bayan kotun koli ya soke hukuncin daureshi na tsawon shekara 12 da aka yanke a watan Disamba, 2019.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotun koli ta warware daurin Orji Uzo Kalu, ta sake shi daga Kurkuku har ya isa gidansa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama