• Labaran yau


  Duba maganin Korona da Gwamnan Bauchi ya ce bai yi nadamar cewa a yi amfani da su ba

  Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammaed ya ce bai yi nadaman gaya wa ma'aikatan lafiya cewa su ba masu cutar korona Chloroquine domin jinyar cutar ba.

  Gwamnan ya yi wannan bayani ne domin mayar da martani ga wadanda ke sukar kalamansa kan maganin cutar korona, wadanda ke ganin kwararru kan harkar lafiya ne kawaai suke da hurumin sanar da maganin jinyar korona.

  Gwamnan ya gaya wa manema labarai cewa ya yi amfani da Chloroquine, Zithromx da Vitamin C ne wajen jinyar kansa lokacin da ya kamu da cutar korona.

  Ya kara da cewa gwamma ya fadi maganin da ya yi amfani da shi wajen jinyar kansa kuma ya warke domin jama'arsa su amfana marmakin a bar masu cutar su yi ta mutuwa.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Duba maganin Korona da Gwamnan Bauchi ya ce bai yi nadamar cewa a yi amfani da su ba Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama