• Labaran yau


  Kashe bakar fata ya jawo kone ofishin yansanda da zanga zanga a biranen Amurka

  Fusatattun masu zanga zanga a Minneapolis na kasar Amurka sun banka wa ofishin yansanda na Precinct wuta yayin da tashin hankali da zanga zanga ya barke a wasu manyan birane na kasar ta Amurka bayan wani dansanda farar fata ya kashe wani bakin fata mai suna George Floyd ranar Litinin.

  An ga taron fusatattun jama'a suna cinna wa ababen kyalkyali masu fashewa wuta, lamari da ya kai ga kone ofishin yansanda a Precinct.

  Fox News ta ruwaito cewa masu zanga zangan sun shiga ofishin yansanda na Precinct da karfe 10 na dare, yansanda da aka girka su a kan rufin ofishin yansandan sun yi kokarin tarwatsa masu zanga zangan da iya abin da za su iya yi, amma masu zanga zanga suka shiga cikin ginin ofishin kuma suka banka masa wuta.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kashe bakar fata ya jawo kone ofishin yansanda da zanga zanga a biranen Amurka Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama