Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya karyata rahoton da jaridar Sahara Reporters ta wallafa a ranar Alhamis kan shugaba Muhammadu Buhari. Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa, rashin kyakkyawan yanayin hanyar sadarwa ya hana shugaba Buhari gabatar da jawabai a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar ta hanyar bidiyo domin kiyaye dokar nesa-nesa da juna.
An gabatar da taron ne kan al'amuran da suka shafi kudi da ci gaban kasa, wanda babban sakataren majalisar, António Guterres ya jagoranta. Sai dai fa jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa, rashin kyakkyawan yanayi na hanyar sadarwa da shugaban Najeriya ya fuskanta tun daga mafarar taron da aka gudanar ta hanyar bidiyo, ya sa bai samu damar cewa uffan ba.
Haka kuma jaridar ta alkanta wannan rahoto da cewa ta kalato shi ne daga rahoton da jaridar The Punch ta wallafa Yayin maryar da martani a safiyar yau ta Juma'a, 29 ga watan Mayu, mai magana da yawun shugaban kasa ya karyata rahoton da jaridar Sahara Reporters ta wallafa.
Cikin sakon da hadimin shugaban kasar ya wallafa da misalin karfe 8.35 a kan shafinsa na Twitter, ya kira jaridar Sahara Reporters da kamfanin kirkirar labarai na karya a kasar. Ya ce "shugaba Buhari ya yi jawabi yayin taron a jiya. Muna wurin kuma duk mun shaida." Domin tabbatar da shaidarsa,
Mallam Shehu ya sanya hoton kanin labarai da jaridar Sahara Reporters ta wallafa tare da hoton taron da aka yi ta hanyar bidiyo wanda ya nuna cewa babu shakka ubangidansa ya halarta. Makonni biyu da suka gabata ne shugaban kungiyar Izala a Najeriya, Shiekh Abdullahi Bala Lau ya karyata labarin mutuwarsa da jaridar Sahara Reporters ta wallafa a shafinta na yanar gizo da kuma Twitter.
A ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu, jaridar ta wallafa rahoton da ya tayar da hankalin kungiyar Jama’atul Izalatul bid’ah wa Iqamatus Sunnah, inda ta ce shugaban kungiyar ya rasu a ranar Asabar. Ta kuma wallafa hotunan jana’iza a shafinta na Twitter tare da hoton gawar da ta ce ta Shiekh Bala Lau ce da aka yi jana’izarsa da safiyar Lahadi. Sai dai a hirar da Sheikh Bala Lau ya yi da sashen Hausa na BBC, ya ce yana nan da ransa cikin koshin lafiya.
Rahotun Legit
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari