• Labaran yau


  An garzaya asibiti da mai martaba Sarkin Rano cikin mawuyacin yanayi

  An garzaya asibiti da Mai Martaba Sarkin  Rano, Dr Tafida Abubakar Ila ll ranar 1 ga watan Mayu sakamakon rashin lafiya.

  Daily Trust ta ce ba a tantance ko rashin lafiyar na da nasaba  da cutar coronavirus ba, amma an kai basaraken Asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke birnin Kano a cikin matsanancin yanayi. Amma sai aka tura su Asibitin kwararru na Nassarawa saboda samun ingantaccen kulawa.

  Wani mai mukamin gargajiya a Masarautar Rano, ya shaida wa manema labarai bisa amintan sirri, cewa an kai basaraken Asibitin AKTH ne  da farko, amma sai aka tura shi Asibitin kwararru na Nassarawa sabo da rashin iskan Oxygen.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An garzaya asibiti da mai martaba Sarkin Rano cikin mawuyacin yanayi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama