Wata Kotu a kasar Ghana ta daure wani saurayi mai suna Derrick Amponsah, tsawon shekara 7 bayan ta same shi da laifin cizon wata yarinya mai shekara 15 yar makaranta a al'aura bayan ya yi mata fyade lamari da ya haifar wa yarinyar da matsanancin zuban jini.
Kafofin labaran kasar Ghana sun labarta cewa lamarin ya faru ne a Manso Yawkrom a Amansie na kudu da ke yankin Ashanti.
Mai gabatar da kara na yansanda Safeto Stephen Ofori ya shaida wa Kotun Bekwai cewa wanda ake zargin ya yi amfani da al'aurarsa, yatsun hannayensa da bakinsa wajen cin zarafi da keta budurcin yarinyar ranar 15 ga watan Aprilu da karfe 11 na safe.
Bayan wanda aka yi kara ya amsa laifinsa a Kotu, Alkalin Kotun ya daure shi tsawon sheekara 7 a Kurkuku.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari