Yanzu yanzu: Mutum 16 sun kamu da cutar coronavirus,jimilla sun zama 305 a Najeriya

Rahotun Legit Hausa

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane goma sha bakwai (17) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Jumaa, 10 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An tabbatar da mutane goma sha shid a(16) sun kamu da #COVID19 a Najerya, 8 a Lagos 3 a Katsina 2 a Abuja 1 a Neja 1 a Kaduna 1 a Anambra 1 a Ondo

“Kawo karfe 9:30 na yammacin 10 ga Afrilu, mutane 305 aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya, an sallami mutane 58, kuma mutane 7 a rigamu gidan gaskiya.“

A yau, Juma'a, ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da kwamitin 'ko ta kwana' da ya kafa a kan annobar cutar covid-19.

A cikin wata sanarwa da shugaba Buhari da kansa ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewa ya na matukar godiya ga kwamitin bisa jajircewarsa a kan aikin da aka dora masa. Kazalika, ya nuna karfin gwuiwarsa a kan cewa kokarin da kwamitin ya ke yi, zai bawa Najeriya damar samun nasara a kan wannan annoba.

"A yau ne kwamitin ko ta kwana a kan shawo kan annobar cutar covid-19 ya kawo min ziyara domin yi min bayani a kan aiyukansu da halin da ake ciki.

"Ina mai farin ciki da godiya bisa jajircewarsu wajen sauke nauyin da aka dora musu. Ba ni da kokonto ko kadan a kan cewa kokarinsu zai bawa Najeriya damar samun nasara a kan annobar," a cewar Buhari.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN