Masoya Abubakar Malami za su yi feshin maganin sauro a shiyar Fada B-kebbi - Habibu Bello

Kungiyar Khadi Malami Matasa Progressive Association Nassarawa 1 Birnin kebbi, manbobinta samari da matasa, wanda shugaban matasa na kungiyar Malam Habibu Bello, zai dauki nauyin yin feshin maganin sauro a shiyar Fada domin taimakon jama'a

Kungiyar ta kuduri aniyar yin aikin feshi a wannan unguwa domin rage tsananin yawan sauro da jama'ar unguwar ke fama da shi kamar yadda Ma;lam Habibu ya shaida mana.

Malam Haboibu Bello ya ce " Za mu fara feshin maganin sauron ne daga Shataletalen Sarki Sir Yahaya, zuwa Shataletalen sabuwar Kasuwa, kuma ta dauke zuwa mahadar hanya ta gidan Dr. Bello, zuwa tsohowar kasuwa, har bayan makarantar Cibiyar Musulunci na Abdullahi Fodio.

An shirya wannan aiki zai sami halartar matasa da masoya tafiyar Abubakar Malami domin ganin an yi nassara bisa tsari da manufa.

Majiyarmu ta ce za a fara gudanar da aikinn ne da karfe 10 na safe ranar Lahadi

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN