• Labaran yau


  Yanzu yanzu: An kwantar da Fraministan Ingila a Asibiti sakamakon cutar coronavirus

  An kwantar da Fraministan kasar Britaniya Boris Johnson sakamakon cutar coronavirus. Dan shekara 55, Johnson ya fitar da sanarwa ranar 27 ga watan Maris inda ya ce sakamakon gwaji da aka yi masa ya nuna ya kamu da cutar coronavirus. Sakamakon haka ya killace kanshi a gidansa da ke Downing Street har tsawon kwana bakwai.

  Wata sanarwa daga ofishi Fraministan ta ce kwantar da Fraministan ba lamarin gaggawa bane, sai dai an yi haka ne domin ya kara samun kulawa.

  An kwantar da Johnson ne a Asibitin NHS da ke birnin London. Sanarwar ta kara da cewa zai kasance a Asibitin har zuwa wani lokaci har sai lafiyarsa ya inganta..

  DAGA ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yanzu yanzu: An kwantar da Fraministan Ingila a Asibiti sakamakon cutar coronavirus Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama