Shugaban kasa ya jagoranci soji zuwa fagen daga sun halaka yan boko haram da kwamanda

Sojin kasr Chadi sun yi wani gagarumin nassara wajen fada da boko haram bayan shugaban kasar Idris Debi, ya jagoranci sojin zuwa fagen daga inda soji suka yaki yan boko haram yayin da suka karbar umarni kai tasaye kuma nan take daga shugaba Debi wanda ke tare da sojin a fagen daga.

Shugaba Debi ya jagoranci sojin ne domin ramuwar gayya bayan yan boko haram sun yi wa sojin kasar Chadi 90 kwanton Bauna suka halaka su.

An gudanar da wannan fada ne a yankin Tafkin Chadi, kuma shugaba Idris Debi ya sha alwashin ganin an kakkabe boko haram daga wannan yanki.

An kama wani kwamandan boko haram tare da tarin makamai.


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN