Miji ya yi kokarin ceton amaryarsa amma ta mutu da mutum 2 a cikin ruwa a jihar Kebbi

Allah ya yi wa mutum uku rasuwa bayan sun nutse a cikin ruwa a garin Ulera da ke gundumar Makawa a karamar hukumar Ngaski da ke jihar Kebbi bayan tahunan Jirgin ruwa da ya dauko su ya lalace a tsakiyar ruwa ranar Asabar da yamma.

Shugaban karamar hukumar Ngaski ya ce " Magidancin yakan dauki iyalansa ya ketara da su zuwa wani gefe idan lokacin kamun kifi ya yi, sai bayan wata uku za su dawo inda suke noma, bayan sun shafe kimanin kilomita ashirin da biyar a  cikin ruwa, sai tahunan jirgin ya mutu kuma ana iska.


" Daga bisani jirgin ya kife a cikin  ruwa, kafin jirgin ya nutse, jama'a da ke ciki suna ihu domin neman agaji, shi mijin matar bai dade da aurenta ba, domin aurensu bai wuce wata uku  ba, kuma su biyar ke cikin jirgin.  Mijin ya yi kokarin ko ta yaya ya tabbatar da cewa sun tsira gabadayansu.

' Ita budurwa daya tun nan wajen ta nutse, mijin ya yi kokari ya kama hannun matarshi, har suka taba tafiya yana iyo rike da hannunta, to kafadarshi na ciwo kuma yana goye da yaro daya da ya hau bayansa yana iyo da su gaba  daya, daga bisani ya fahimci cewa tabbas zasu rasa rayuwarsu, sai matar ta ce wa mijinta, wane ka sake ni in mutu, ka yi hakuri ka sake ni in mutu, ita ta galabaita, shi kuma mijin ya gaji, sai ya fahinci cewa dukkansu zasu iya mutuwa a wannan yanayi.

" Dole  sai ya yi hakuri ya sake hannunta, wani jirgi da ya kawo masu dauki ya kusan isowa sai matar ta nutse a cikin ruwa tare da jirgin, shi kuma mijin ya yi kokari ya tako tudu tare da yaro da ya rike bayanshi, kenan da yaro daya da budurwa, tare da matar aure daya wacce matar mutumin ce su ne Allah ya sa suka easa rayukansu.

" Bayan dabin ya faru, na isa bakin rafin tun karfe shida na yama, an fito da gawa daya a gaban idona, kuma an fito da gawa  na macen daya, wannan shi ne tabbacin abin da ya faru: Inji Hon Abdullahi Buhari Warrah shugaban karamar hukumar mulki ta Ngaski a jihar Kebbi.

Hotuna: Lawal Shehu

Rahotun Isyaku Garba Zuru

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN