• Labaran yau


  Duba abin da ya faru bayan yansanda 2 sun yi dambe da juna a bainar jama'a

  An kori wasu yansanda biyu da aka ga suna dambe da juna a wani faifen bidiyo a jihar Edo.

  Wadanda aka kora daga aiki su ne  F/NO 41112 CPL Ozimende Aidonojie da F/NO 516384 PC Salubi Stephen bayan an kama su, aka gurfanar da su a Kotun yansanda da ake kira Orderly Room a Shelkwatan yansanda na jihar Edo, daga bisani aka zartar masu da hukuncin kora daga aiki bayan an kama su da laifin yin dambe a bainar jama'a.

  Yansandan sun dambace juna ne a garin Ebele da ke karamar hukumar Igueben na jihar Edo. Sanarwar koran yansandan daga aiki ya fito ne a shafin hukumar yansanda na Twitter.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Duba abin da ya faru bayan yansanda 2 sun yi dambe da juna a bainar jama'a Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama